Harin kuskure ya kashe sojojin Afganistan
October 1, 2017Talla
Ma'aikatar tsaron Afganistan dai sun tabatar da aukuwar harin, inda suka ce harin ya faru ne a lokacinda sojojin da ke farautar 'yan tawayen Taliban da ke samun mafaka a yankin da sojojin kasa ke aikin bincike. Wannan harin na zuwa ne bayan da yankin ke ci gaba da fuskantar artabu mai tsanani a tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawayen Taliban.
Harin dai ya faru ne a dai dai lokacin da shugaban kasar Afganistan Ashfar Gani ya gana da hafsan hafsoshin rundunar sojojin kasar Pakistan Janar Qamar Javed Bajwa a birnin Kabul, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi inganta tsaro a tsakanin kasashen biyu da kuma yunkurin farfado da ma'amala a tsakanin juna.