Indonesiya ta fuskanci harin ta'addanci
January 14, 2016wadannan hare-haren dai ana kyautata zaton an tsara kai su ne a lokaci guda. Wani shaidan gani da ido ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Amirka na Associated Press cewa wasu 'yan kunar bakin wake uku ne suka tarwatsa kansu a wani shagon sayar da kofi yayin da wasu mahara biyu kuma suka kai hari ofishin 'yan sanda da ke kusa da shagon. Harin dai na zuwa ne bayan da kungiyar 'yan ta'addan IS ta yi barazanar cewa za ta sanya kasar ta Indonesiya cikin jerin kasashen da take kaiwa hare-hare. Wani shaidan gani da ido daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ma ya shaidar da cewa yaga gawarwaki uku yayin da kuma ake ci gaba da jin karar harbe-harben bindiga. Ga dai ta bakin wani shaidan gani da ido mai suna Irfan a hirarsu da 'yan jarida:
Ya ce: "Eh naji karar fashewar wani abu sau uku"
A baya ma dai Indonesiya da ke zaman kasar da Musulmi suka fi yawa a duniya, ta sha fuskantar hare-haren ta'addancin daga kungiyar tsagerun Jemaah Islamiyah.