Harin tashin bom a birnin Tel-Aviv na Isra'ila
November 21, 2012
Rahotani daga birnin Kuddus na Isra'ila sun tabbatar da aukuwar wani harin tashin bom a wata motar supurin jama'a da aka kai a wannan safiya a birnin Tel-Aviv na kasar inda kimanin mutane 10 ne suka samu munayen raunika,to saidai babu wasu rahotanin da suka bayana adadin wadanda suka mutu. Wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da sakateriyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton da sakteriyar majalisar dinkin duniya Ban ki-moon ke tautaunawa da hukumnomin Isra'ila a matakin neman tsagaita wuta a yakin da ake gobzawa da Isara'ila da palastinawan yankin gaza mako daya kenan. Jim kadan bayan bayana wannan sanarwar harin murana ta kece a yankunan Gaza,kamun daga bisani kungiyar Hamas ta bayana daukar alhakin harin.
A dai bangare hukumomin Iran sun kira kasashen laranawa da su bi sahunsu gurin taimakawa mayakan Gaza da makamai.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohamad Nasiru Awal