Jimamin kisan jami'an 'yan sanda
November 1, 2021Talla
An kai harin ne a yankin arewacin kasar Burkina Faso, inda 'yan sanda biyar suka rasa rayukansu a yayin artabu a tsakanin jami'an 'yan sandan da 'yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata. Sanrwar ma'aikatar tsaron kasar da ke yankin Sahel bayan tabbatar da labarin, ta ce jami'an sun yi nasarar halaka goma sha biyar daga cikin maharan da suka kai harin.
Lamarin ya auku ne a Sourou, yankin Burkinan da ke kusa da kan iyaka da kasar Mali, inda mayakan IS da suka yi kaurin suna, ke kai hare-hare ba kakautawa duk kuwa da kokarin manyan kasashen yamma na kai ma kasashen na Sahel taimako daga hare-haren da suka hana yankin zaman lafiya dama ci gaba. Mutum sama da miliyan daya hare-haren ta'addanci suka raba da muhallinsu a Burkina Faso.