1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin 'yan Taliban akan cibiyar al'adun Birtaniya a Afghanistan.

August 19, 2011

Wasu 'yan ƙunar baƙin wake 'yan Taliban sun afkawa cibiyar al'adun Birtaniya a Afghanistan inda aƙalla mutane takwas suka mutu wasu kuma suka sami raunuka.

https://p.dw.com/p/12JQV
Ofishin jakadancin Birtaniya a Afghanistan da aka kaiwa hari.Hoto: AP

Wasu 'yan ƙunar baƙin wake 'yan Taliban sun kai hari cibiyar al'adun Birtaniya da kuma ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya dake birnin Kabul a Afghanistan. Harin ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane takwas da kuma jikata wasu mutanen goma. Aƙalla bama bamai uku ne suka faɗa cibiyar al'adun Birtaniyan yayin da a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniyar kuma aka yi musayar wuta da 'yan bidigar. Ƙungiyar Taliban ta ayyana ɗaukar alhakin kai hare haren biyu waɗanda suka zo a daidai ranar da ake hutun zagayowar samun 'yancin ƙasar daga turawan Birtaniya a shekarar 1919.

Afghanistan Taliban
'Yan Taliban a AfghanistanHoto: AP

Wani mai magana da yawun ƙungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters ta wayar tarho cewa sune suka kai harin amma bai baiyana adadin 'yan ƙunar baƙin waken da suka kai harin ba. Ofishin jakadancin Birtaniya da kuma rundunar tsaro da kiyaye zaman lafiya ta NATO duk sun tabbatar da aukuwar harin. Hakan dai na zuwa ne wata guda bayan da NATO ta miƙa ragamar tsaron yankuna da dama ga dakarun tsaron Afghanistan.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita Umaru Aliyu