Harkokin gudanawar gwamnatin Amirka sun tsaya ciki
January 20, 2018Talla
Bangarorin jagorancin Amirkar sun gaza cimma matsaya a kan samar da kudaden tafiyar da gwamnati da kuma matsalar bakin haure, abin da ya fito da bambancin da ke a Amirka a yanzu. Lamarin ya tilasta rufe wasu harkokin da ake ganin ba su da muhimmanci, kuma babu wani da ya san halin da ake ciki dangane da musayar yawun kyautata lamarin.
Gardamar kuwa na faruwa ne shekara guda cif da kama madafun iko da shugaba Donald Trump ya yi.
Wannan ne dai karo na farko tun bayan irinsa da aka gani cikin watan Oktobar shekarar 2013, inda harkokin gudanar da Amirka suka yi tsayuwar kwanaki 16 cur.