Durkusar da harkokin gwamnati a Amirka
December 22, 2018Talla
'Yan majalisar dai za su sake zama a wannan Asabar a kokari na warware takaddama da ke tsakaninsu da Shugaba Trump kan bukatunsa da ma neman su ba shi dama ya kashe kudade da yawansu ya kai Dala miliyan dubu biyar. Kudaden da zai yi amfani da su wajen gina katanga tsakanin Amirka da kasar Mexiko.
Kimanin kashi daya cikin kashi hudu na harkokin gwamnatin ta Amirka za su tsaya, abin da zai shafi ma'aikatun gwamnati tara da dubban daruruwan ma'aikata, saboda wasu sai dai su yi aiki ba tare da biyansu albashi ba, wasu kuma su tafi hutu ba albashi, matakin da ke zuwa kwanaki kadan kafin bikin ranar Kirsimeti.