Hatsarin mota ya kashe mutane a Kenya
October 10, 2018Talla
Alkaluman mahukunta na cewa akalla mutum 42 ne suka mutu a hadarin da motar kira bas ta yi a yankin yammacin kasar.
'Yan sanda sun ce akwai yiwuwar samun karuwar wadanda za a rasa, saboda munin hadarin wanda ya kai ga kwaye rumfar motar.
Motar dai na kan hanyarta ne ta zuwa Kakamega daga Nairobi, tana kuma dauke ne da fasinjoji 52.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce motar ta tintsire ne, kuma ya zuwa yanzu ba a kai ga tabbatar da musabbabin hadarin ba.
Kimanin mutum dubu 12 ne ke mutuwa a duk shekara a Kenyar, sakamakon hadarin ababen hawa.