Haɗin kai a tsakanin Isra'ila da Jamus
January 31, 2011Majalisun ministocin Jamus da na Isra'ila za su gudanar da zaman haɗin gwiwa yayin da Tawagar ministocin Jamus a ƙarƙashin jagorancin shugabar gwamnatin ƙasar Angela Merkel za ta sauka a birnin Qudus. A lokacin zaman haɗin gwiwar majalisun biyu, wadda za ta kasance makamanciyar ta karo na uku, gwamnatocin ƙasashen biyu za su tattauna hanyoyin inganta dangantaka a tsakanin su ta fannin shawo kan matsalar sauyin yanayi, da rage yawan hayaƙi mai guba, da kuma musayar bada horo ga matasa.
Hakanan kuma ana sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu game da ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya da yaƙi ci yaƙi cinyewa, da kuma yanayin rikicin da yake faruwa a ƙasar Masar da ke makwabtaka da ita Isra'ilar.
Akan wannan matsalar ce kuma tsohon ministan tsaron Israila, Shaul Mofaz, ya bayyana cewar, tilas ne duniya ta ɗauki matakan warware rigimar da ke tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa cikin gaggawa a yanzu:
"A yau zamu iya fahimtar cewa abin da muka gaza cimma lokacin da muka fi samun kwanciyar hankali shi ne samar da zaman lafiya tsakanin mu da Falasɗinawa. Amma ya zama dole a yi hakan yanzu saboda guguwar canjin nan da ke kaɗowa a yankin ta na iya cimma kowace ƙasa hatta wadda ta ke da zaman lafiya a yanzu"
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal