1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɗin kan ƙasashen gabashin Afirka

December 1, 2013

Ƙasashen gabashin Afirka sun cimma daidaiton samar da takardar kuɗi na bai ɗaya, domin ƙarfafa cuɗanya da juna.

https://p.dw.com/p/1ARGf
East African Presidents, from left to right, Jakaya Kikwete of Tanzania, Uhuru Kenyatta of Kenya and Yoweri Museveni of Uganda pose for a group photograph in Munyonyo, near Kampala, in Uganda, Saturday, Nov. 30, 2013. The leaders gathered at a meeting of the East African Community (EAC) to discuss a possible future regional monetary union, amongst other regional economic and security issues. (AP Photo) / eingestellt von ml
Hoto: AP

Ƙasashe biyar mambobin Ƙungiyar Ci -gaban Tattalin Arzikin Gabashin Afirka sun cimma matsaya dangane da buƙatar samar da takardar kudi na bai ɗaya a tsakaninsu. A dai wannan Asabar ( 30. 11. 13) ce shugabannin ƙasashen Kenya, da Yuganda, da Tanzaniya, game da Rwanda, da kuma Burundi suka sanya hannu a kan yarjejeniyar, yayin wani taron da suka gudanar a birnin Kampala na ƙasar Yuganda. A cikin wata sanarwar da suka fitar bayan taron, shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, wanda kuma har ila yau ke jagorantar Ƙungiyar Ci-gaban Tattalin Arzikin Gabashin Afirka, ya ce a yanzu sun buɗe ƙofar cika alƙawarin haɗe wa wuri guda, wadda za ta ba da damar gudanar da harkokin kasuwanci da na zuba jari ba tare da wata matsala ba, kana da sauƙaƙa wa masu zuba jari na ƙetare ma gudanar da harkokin kasuwancinsu. Ƙungiyar, wadda ƙasashen yankin suka samar da ita kimanin shekaru 13 da suka gabata dai, tuni ta yi nasarar samar da kasuwa ta bai ɗaya da kuma gamayyar harkokin kwastam na bai ɗaya. Ta kuma bayyana ƙudirin samar da takardar kuɗi ta bai daya cikin tsukin shekaru 10 masu zuwa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane