Himma dai Matasa: Matashin makeri
May 5, 2021Wannan matashi dai ya samu karbuwa a wajen jama'a sakamakon ingancin aikinsa da kuma yadda ake masa kallon wannan matashi abun misali ga matasa 'yan uwansa. Matashi Abdou Hassane mai shekaru 32 a duniya ya soma koyon aikin hannu ne tun yana dan karami, inda daga bisani abokai suka ba shi shawarar zuwa kasar Libiya domin ci-rani. Ya ci gaba da wannan aiki nasa a can kasar ta Libiya tare da samun karin ilimi a kan sana'ar ta kere-kere ta hanyar hada karfe da karfe yana yin walda.
Duk da cewa ya koma can kasar Libiya da sana'ar tasa, ya yanke shawarar koma wa gida Nijar. Abdou ya bayyana cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu a sana'ar tasa, koda yake akwai matsaloli na karancin kayan aiki. Matashin ya yaye matasa da dama da suka koyi aiki a karkashinsa, wanda yanzu haka suma suke cin gashin kansu, kana yanzu yana da yara biyu da ke koyon aiki a karkashinsa. Himma dai 'yan magana suka ce ba ta ga rago, domin kuwa Abdou Hassane na gudanar da wannan sana'a tasa cikin himma. Baya ma ga gadajen karfe da shagon tafi da gidanka, yana kuma kera murhun zamani na dafuwar abinci da ake iya sa misagawayi ko kuma iskar gas.