1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hidindimun babban zabe a Senegal

Mouhamadou Awal Balarabe MA
February 5, 2019

A kasar Senegal, yakin neman zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 24 ga wannan wata na Fabrairu ya kama hanyar shiga mako na farko, zaben da Shugaba Macky Sall ke neman wa'adi na biyu.

https://p.dw.com/p/3CjoN
Senegal Wahlplakat von Präsident Macky Sall
Hoto: DW/R.S. Adé

'Yan takara biyar ne suka samu tikitin tsayawa takarar shugabancin Senegal ciki har da Madicke Niang mai shekaru 65 wanda kuma yake da kusanci da tsohon shugaba Abdoulaye wade. Sai tsohon Firaminista Idrissa Seck, da Ousman Sonko tsohon jami'in kwastom da aka kora daga aiki shekaru biyun da suka gabata. Da 'dan majalisa Issa Sall da kuma Shugaba Macky Sall.

Babu wani abin da ke daukar hankali a kanun labaran kasar a yanzu illa manyan gine-ginen da gwamnatin Macky Sall ta kaddamar a Senegal. A kowane titi na Dakar da sauran biranen kasar ma, ana samun hotunan tallar shugaban kasa a manyan allunan da ke dauke da alamomin ci gaban da ya samar. Wannan yana nuna cewar daga cikin dukkan shugabannin kasar da Senegal ta samu tun bayan samun ‘yancin kanta daga turawan Faransa, ba wanda ya kama kafar Macky Sall a fannin aikinshi, a cewar Babacar Tamba, wani dan kasuwa da ke Guediawaye, daya daga cikin wuraren da ke kusa da babban birnin kasar.

Shugaba Macky Sall na kasar Senegal
Shugaba Macky Sall na kasar SenegalHoto: Imago/Xinhua/Lv Shuai

Makonni uku 'yan takarar za su shafe suna tallata manufofinsu, kasancewar akwai wadanda ba su da gogewa a fannin shugabanci irin su Ousman Sonko. Sai dai wadanda suke hamayya da Shugaba Macky Sall na kushe ayyukan da ya gudanar a shekaru bakwai na mulki. 

 

Baya ga haka, akwai ginin sabon gari mai suna Diamniadio da aka bijiro da shi, da kuma layin doga da ke hade garin da Dakar babban birnin Senegal. Sai dai Ndene Sarr, dan asalin Diamniadio bai gamsu da kamun ludayin Macky Sall ba, yana mai cewar farfaganda ce kawai.

Ko da yake ba a kammala wasu daga cikin manyan ayyukan da Macky Sall ya fara ba, amma magoya bayansa suna dogaro kan ayyukan raya karkara da ya gudanar wajen gudanar da yakin neman zabe, inda ya wadata kauyuka da wutar lantarki da gyara hanyoyi tare da samar musu da zuwa mai tsabta.