Hizbollah ta maida wa Isra'ila martani
August 25, 2019Talla
Jagoran kungiyar ta Hizbollah Sheikh Hassan Nasrallah, ya ce harin da jirage marasa matuka mallakin Isra'ilar suka kai wani yanki na Beirut na kasar Labanan wani hadari ne babba. Kungiyar ta ce harin ya lalata tashar watsa labarunta da ke a kudancin birnin na Beirut.
Tun da farko Firaministan kasar Labanan Saad Hariri ya bayyana harin na Isra'ila a matsayin wani kokari ne na haddasa husuma tsakanin kasashe. Iran dai na goyon bayan kungiyar da 'ya'yanta ne galibin mazauna a Beirut.
Harin na kuma zuwa ne bayan dakarun Isra'ila sun ce wani jirginsu ya kai hari kan sojojin Iran da mayakan tawayen Shi'a, a kusa da Damascus babban birnin kasar Siriya. Jagoran na Hisbollah Hassan Nasrallah ya ce harin na Siriya ya kashe masa mutane biyu.