1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW ta koka da yawan yara da yaki ke ci a duniya

July 30, 2019

Sama da yara dubu 12 ne aka kashe a bara kadai sanadiyyar rigingimun da ke faruwa a wasu sassa na kasashen duniya, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/3N1cE
Kindersoldat Südsudan
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Bor

Wasu alkaluma da Majalisar Dinkin duniya ta fitar, ya nuna cewar sama da yara dubu 12 ne aka kashe a bara kadai, sanadiyyar rigingimun da ke faruwa a wasu sassa na kasashen duniya.

A cewar rahoton kasashen da lamarin ya fi kamari a cikin su, sun hada ne da Afghanistan da Siriya da Yemen da ma yankin Falasdinu.

Cikin wasu kasashen Afirka ma akwai Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da kasar Libiya da Mali da Najeriya da Somaliya da kuma Sudan.

Akwai kuma matsalar nan ta tilasta masu shiga aikin soja a wasu kasashen, wanda Majalisar Duniyar ta ce ke nakasa rayuwar yaran.

Wasu dubbai daga cikin su ma na fama da raunuka sanadin rikice-rikicen.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta HRW ta yi tir da lamarin, musamman a Yemen inda Saudiyya ke jagorantar yaki.