1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar Unicef ta nemi gudummawar masu gidan rana

Ibrahim SaniJanuary 24, 2006

Unicef ta dukufa ka´in da na´in wajen tallafawa kana nan yara dake fama da matsaloli daban daban a duniya

https://p.dw.com/p/BvTx
Hoto: AP UNICEF

Ya zuwa yanzu dai asusun tallafawa kana nan yaran na Mdd, yace yana neman gudummawar dalar Amurka miliyan 805 ne don tunkarar wasu matsaloli da suka danganci yara a kasashe daban daban na duniya.

Hukumar ta Unicef, ta tabbatar da cewa a yanzu haka akwai matsaloli 29 da yara ke fama dasu a kasashe daban daban na duniya, wadanda suke bukatar taimakon gaggawa.

Babban batu da zata fi mayar da kai wajen kashe wadannan kudade idan an samu a cewar hukumar ta Unicef, sun hadar da samar da abinci mai gina jiki da kyakkyawan ruwan sha da kuma ingantaccen ilimi ga yara kana nan a kasashe daban daban na duniya.

Faruwar wadannan matsaloli ga yaran a cewar babban dakartar hukumar, wato Ann Veneman ya samo asali ne a sakamakon ci gaba da faruwar rikice rikice a wasu kasashe a duniya a hannu daya kuma da cututtuka da rashin abin ci mai gina jiki.

Daga cikin jumlar kudaden da hukumar ta nema, tace zata kashe a kalla miliyan 331 ne gada yawa daga cikin yara a kasar Sudan, wadanda rikice rikicen yankin Darfur ya jefa a cikin hali na kaka ni kayi.

Rahotanni dai sun nunar da cewa a yanzu haka akwai yara kusan miliyan daya da digo hudu da rayuwar su ke cikin mawuyacin hali a kasar ta Sudan a sakakamon rikice rikice da tashe tashen hankula dake ci gaba da wanzuwa a yankin na Darfur.

Ya zuwa yanzu a cewar hukumar ta Unicef, ako wace shekara yara masu shekaru kasa da biyar ne kusan dubu dari a kasar ta Sudan suke rasa rayukan su daga wasu cututtuka da za´a iya maganin su.

Ba a da bayan kasar ta Sudan , hukumar ta Unicef take akwai kuma daruruwan yara dake cikin garari a wasu kasashen dake gabashi da kuma kudancin nahiyar ta Africa.

Har ila yau, akwai kuma yara da yawa da a yanzu haka ke fuskantar barazana a wasu kasashe na tsakiya da gabashin turai, a sakamakon kana nan rikice rikice da kuma bala´oi iri daban daban daga indallahi.

Bugu da kari, hukumar ta tallafawa kana nan yaran ta tace a kudanci da gabashin yankin Asia ma akwai miliyoyin yara da yunwa kewa barazana, sakamakon faruwar fari da tsunami. Sannan a hannu daya ga rashin kyakkyawan muhalli da kuma abubuwan more rayuwa da yaran ke fuskanta.

A karshe rahoton na Unicef ya kuma tabbatar da cewa rikici dake ci gaba da wanzuwa a tsakanin Israela da Palasdinawa na dada jefa kana nan yara na yankin cikin mawuyacin hali na rayuwa.