1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Sudan ta Kudu sun rufe wani gidan rediyo

August 19, 2014

Kwamitin da ke ba da kariya ga 'yan jarida ya bayyana cewar mahukunta sun rufe wani gidan rediyo a Juba babban birnin ƙasar.

https://p.dw.com/p/1CwzI
Südsudans Präsident Salva Kiir Mayardit
Hoto: Reuters

Kwamitin ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar cewa jami'an tsaro sun mamaye gidan rediyon Bakhati a ranar Asabar, su ka yi awon gaba da ma'aikata guda huɗu ciki kuwa har da daraktan labarai na wannan gidan rediyo wanda har yanzu ke hannun mahukunta.

Wannan sanarwa dai ta ambato cewar Ateny Wek, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa ya ce gidan rediyon na yaɗa shirye-shiryen da suke barazana ga tsaron ƙasar, inda ya ke bayyana cewar jami'an tsaro na ɓangaren gwamnati su ke daɗa rura wutar rikici yaƙin ƙasar.

Mawallafi : Yusuf Bala
Edita : Abdourahamane Hassane