1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa kan wasu 'yan IS 40 a Iraki

Gazali Abdou TasawaFebruary 18, 2016

Kotun kasar Iraki ta yanke hukunci kisa kan wasu mambobin Kungiyar IS 40 bisa laifin aikata laifin kisan wasu daruruwan sojojin gwamnati a shekara ta 2014.

https://p.dw.com/p/1HxuH
Syrien Kämpfer Islam Armee Jaish al-Islam Schatten Silhouette
Hoto: Getty Images/A.Almohibany

Kakakin kotun kolin kasar ta Iraki Abdoul Sattar al-Birkdar ya bayyana cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan da ta sami mutanen 40 da laifin aikata ta'addanci. Amma kuma ta saki wasu mutanen bakwai bayan da aka kasa samu kwararran hujjoji na aikata laifi.

Kisan wasu sojoji kimanin dubu da 700 da mayakan Kungiyar IS suka yi a shekara ta 2014 a lokacin da suke kokarin tserewa daga barikin sojan birnin Tikrit ya kasance wani abin misali, na munmunan halin Kungiyar IS da kuma karan tsanar da suka dora wa 'yan Shi'a al'umma mafi rinjaye a kasar ta Iraki.