1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hulɗa tsakanin Sudan ta Kudu da Keniya

January 26, 2012

Ƙasahen guda biyu sun rataɓa hannu akan wata yarjejeniya ta gina wani bututun man fetur da zai riƙa jan man daga juba zuwa garin Lamu da ke gaɓar kogin ruwayen Keniya

https://p.dw.com/p/13q9G
epa02556888 First Vice President of Sudan and President of the Government of Southern Sudan Salva Kiir Mayardit waves to supporters after the announcement of preliminary results of the recent independence referendum in Juba 30 January 2011. Just short of 99 per cent of Southern Sudanese voted to secede from the north and form an independent state. EPA/PHILIP DHIL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Salva Kiir na Sudan ta kuduHoto: picture alliance / dpa

Fraministann ƙasar Keniya ne Raila Odinga ya sanar cewar za a ƙaddamar da aikin a ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙasahen biyu.aikin wanda za a yi shi a cikin shekaru ukku wanda zai ci biliyoyin kudi zai ba da damar da isar da man fetur ɗin na Sudan ta Kudu daga juba zuwa garin Lamu inda daga can za a riƙa fitar da man zuwa ƙasashen waje.

Tun farko man fetur ɗin na ƙasar Sudan ta Kudu a da ya na bi ta hanyar maƙobciyar ƙasar wato Sudan zuwa ƙasashen waje,kafin daga bisanni hukumomin su gano cewar maƙobciyar ƙasar ta Sudan na yin amfani da wannan dama domin sotar masu man akan wasu kuɗaɗen fansa na fito .

Taƙaddama tsakannin Sudan ta Kudu da Sudan akan kuɗaden fito na man fetur

bAbinda ya sa ma gwamnatiin ta Kudanci ta ba da sanarwa dakatar da aikin haƙo man fetur da ya ke yi yin magana a gaban majajalisar dokokin ƙasar shugaba Salva Kir na Sudan ta Kudu ya tabatar da abinda ya kira sotar ɗanyan man fetur da hukumonmin Sudan suke yi.''Ya ce sun gina bututu ne kwai domin juya akalar man mu wanda a kowace rana suke soce kusan ganga dubu 125, ya ce abinda ya janyo mana koma baya akan sha'anin tattalin arziki ya ce ba zamu yardda ba zamu ɗau duk matakan da suka dace na kawo ƙarshen wannan matsala''An shirya shugaba salva Kir da shi da Umar Hassan El Beshir na Sudan zasu gana a birnin Addis Ababa na Habasha domin warwware wannan matsala.Ko da shi ke ana gani cewar ya na da matuƙar wahala a cimma daidaituwar baki tsakanin sasan biyu ,to amma masu yin sharhi akan al'amura na hasashen cewar tilas ne ƙasashen biyu su zauna su tattauna

Omar el Bashir da Salva Kiir Mayardit
Omar el Bashir da Salva Kiir MayarditHoto: picture-alliance/dpa

David Sheen wani masani ne akan ƙasashen gabashin yankin Afirka da ke a jamai'ar George Washinton a Amirka.'ya ce yankin arewacin na Sudan na fuskantar matsi na tattalin arziki sannan su kuma Kudanci na buƙatar ɗauki domin rage yawan kuɗaɗen fiton da su kan biya,ya ce dole ne sasan biyu su cimma wata tsayayyar magana domin ci gaba da gudanar da aikin ta yadda ko wane daga cikin su zai amfana, ya ce dukannin su ,su biyu ko wane zai wahala idan ba a cimma wani shiri ba.

Tattalin arzikin Sudan ta Kudu zai fiskanci koma baya, saboda dakatar da aikin haƙo man fetir

A kowacce rana a lisafin da aka yi a can baya ƙasar ta Sudan ta kudu na haƙo gangar ɗanyan man fetur kimanin dubu 350 kuma ƙasar china ita ce kasa ta farko da ke sayan man. Sannan a yanzu dangane da wannan yarejeniya da aka cimma tsakanin Keniya da Sudan ta Kudu ba shakka ita ma Keniyar zata samu nata rabon ta Robert Shaw masanni ne akan tattalin arziki ne ƙasar Keniya.

ARCHIV Südsudan schließt eigene Verträge zur Ölförderung ab
Hoto: AP

''ya ce Keniya ta riga ta ƙaddamar da irin wannan aiki a wasu ƙasahen gabashin Afirka za ta ci moriya idan har aka kasa lamarin tare da wasu ƙasahen gabashin nahiyar wajan haƙon man''.To sai dai a halin yanzu babbar ayar tambayar da akan iya azawa shi ne cewar ina wannan ƙasa da ta samu yanci a ƙasa da shekara guda zata samar da mafi yawan kuɗaɗenta na shiga bayan da ta rufe rijiyoyin man fetur ɗin da ta ke haƙowa har kusan 900 saboda rikicin da take yi da Sudan.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu