1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Najeriya na murkushe 'yan ta'adda

Ramatu Garba Baba
August 13, 2021

Rundunar sojojin Najeriya ta yi ikirarin samun nasara a fadan da take da masu gwagwarmaya da makamai da suka hana zaman lafiya a wasu jihohin kasar.

https://p.dw.com/p/3yxG5
Nigeria | Präsident Muhammadu Buharitrifft neue Militär Chefs in Abuja
Hoto: Ubale Musa/DW

A wani sabon rahoto da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce, dakarunta sun yi nasarar kashe 'yan bindiga fiye da (123)  tare da kwace makamai da kuma lalata duk wasu kafafen da ke taimaka musu wajen kai hare-hare kan jama'a, mayakan da rundunar ta ce ta samu galaba a kan su sun hada dana Kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da kuma 'yan bindigan da suka addabi wasu jihohin arewacin Najeriyar.

Rundunar ta baiyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis, inda ta saba fidda rahoto kan irin nasarorin da ta ke samu kan masu tayar da kayar bayan. Sai dai, rahoton, ya ci karo da koken jama'a a arewacin kasar da ke ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga masu satar mutane don neman kudin fansa, yanzu haka, akwai dalibai sama da dari da aka yi garkuwa da su daga makarantun kwana, da ke hannun 'yan bindiga.