1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

IMF: Sauyin yanayi na kara rikici da talauci

Abdullahi Tanko Bala
August 30, 2023

Wani sabon rahoto da asusun bada lamuni na duniya IMF ya fitar ya ce akwai yiwuwar sauyin yanayi ya haifar da karin mace mace da kuma rikice rikice.

https://p.dw.com/p/4Vl7k
Hoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Tuni dai aka fara ganin bambance bambance na tasirin sauyin yanyin a kasashen da ke fama da yake-yake wadanda kuma ke da rauni wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayin a cewar rahoton na IMF.

Rahoton ya ce a wasu kasashen da suka fi fuskantar barazanar tashin hankali, lamarin ya sa basa iya tunkarar matsalar wadda tun shekarar 1980 ta ke aukuwa akalla sau daya bayan duk shekaru hudu yawanci a kasashen Afirka.

Asusun bada lamunin na duniya IMF ya yi kira ga kasashen da ke fuskantar barazanar sauyin yanayi su bullo da ingantattun da suka hada da tsarin bunkasa noma mai jure wa sauyin yanayi da kara yawan kudade wajen magance matsalolin muhalli.