Siriya: Ko zaman lafiya zai dore a yanzu?
December 11, 2024Rikicin cikin gida ko dai na siyasa ko na addini a tsakanin kungiyoyin tawayen da suka kifar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya, ya sanya ana ci-gaba da aza ayar tambaya kan yadda kungiyar 'yan tawayen HTS da ta taka rawa wajen kawo karshen tsohuwar gwamnati da kuma kungiyar Kurdawan Siriya za su sulhunta kansu a yanzu. An dai yi ta tsallen murna, a lokacin da shugaban 'yan tawayen Siriya Abu Mohammed al-Jolani ke gaisawa da jama'ar da suka yi gangami a masalacin Umayyad yayin da ya yi jawabi a karon farko bayan da kungiyarsa ta Hayat Tahrir-al-Sharm wato HTS ta kwace iko da babban birnin kasar Damascus. Jolani dai tsohon dan kungiyar al-Qa'ida ne da Amurka ta ayyana a matsayin kungiyar 'yan ta'adda kuma haryanzu yana cikin wadanda take neman ruwa a jallo, tare da sa tikyucin kudi har dala biliyan 10. A bayan-bayan nan ne ya koma amfani da sunansa na asali Ahmad al-Sharaa kana ya koma sa kakin soja maimakon shiga irin ta 'yan ta'adda, lamarin da ake gani yana yi ne domin a kalle shi a matsayin sahihin dan siyasa da kuma kokarin nunawa duniya cewa ba shi da tsattsaurar ra'ayi. Jolani ne ya kafa kungiyar HTS a Arewa maso Yammacin Lardin Idlib na Siriya, ya asassata har ta zama babbar kungiyar 'yan tawaye a yankin. A lokacin ya fara jagorantar kungiyar, ya yi ikrarin cewa ba ya shirin tirsasa tafiyar da harkokin kasar kan tafarkin shari'ar Musulumci a kan wasu addinan da kuma kabilu tsiraru.
Kawancen kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a Siriya, sun samo asali ne daga babbar gamayyar kungiyar 'yan tawayen Free Syrian Army da wadanda suka sauya sheka suka kafa ta a shekarar 2011. Kungiyar tawayen na kunshe ne da kungiyoyi da ke adawa da gwamnati masu dauke da makamai kuma ke samun goyon bayan Turkiyya, sai dai dukannin wadannan kungiyoyin na da mabanbamtan ra'yoyi kan abubuwan da suka shafi addini da siyasa. A gefe guda suma kungiyoyin Kurdawa sun yi ta kakkabo mutun-mutumi da kuma Fastocin da aka kafa na Shugaba Assad a Siriyan, yayin da jama'a ke ci gaba da bukukuwan jin dadin kawo karshen mulkin kama karya na tsawon shekaru 24 a kasar. Tun dai a shekarar 2015, dakarun Kurdawa da ke da rinjaye ke jagorantar wani yankin da ke cin gashin kansa a arewacin Siriya. Tare da hadin gwiwar Larabawa da wasu kananan kabilu sun kafa kungiyar 'yan tawayen Syrian Democratic Forces, kungiyar 'yan tawayen da aka fadada ta a lokacin yakin basasa kana take samun goyon bayan Amurka. Sai dai duk da cewa suna raba abokin gaba guda ne wato hambararren Shugaba Assad da kuma gwamnatinsa, wadannan kungiyoyin Kurdawan na nuna kyama ga makwabciyarsu Turkiyya. Gwamnatin Turkiyyan, ta kaddamar da hare-hare a kansu a 'yan shekarun baya-bayan nan. A yanzu dai, dukkannin kungiyoyin sun taru wajen kawo karshen mulkin shekaru 24 na Bashar al-Assad. Koda yake ana nuna fargaba kan fadan cikin gida tsakanin kungiyoyin 'yan tawayen, wanda ka iya zama kalubale ga makomar kasar Sham wato Siriya.