1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta tsaurara matakan tsaro a birnin Hyderabad

August 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuD9
Bayan munanan hare haren bama-bamai da aka kai kan birnin Hyderabad mai miliyoyin mazauna dake kasar Indiya, hukumomin tsaro na cikin shirin ko takwana. An yi kira ga al´uma da su kasance masu lura da dukkan abubuwan da ka je su komo kana kuma su guji zuwa wuraren taruwar jama´a. Alkalumman da ´yan sanda suka bayar na nuni da cewa mutane kimanin 42 suka rasu sannan wasu dama suka samu raunuka sakamakon hare haren na jiya asabar wanda aka kai kan ´yan kallo a wani wurin wasan nune-nunen hasken lesa da kuma kan wata mashaya. Hukumomin Indiya na zargin wata kungiyar musulmi ´yan ta´adda da hannu a wannan aika-aika. Ana yawaita samun tashe tashen hankula tsakanin ´yan Hindu da Musulmi a birnin Hyderabad. A cikin watan mayu mutane 11 suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai wani masallaci dake birnin.