Hukuncin kisa kan wani Malami a Indonesiya
June 22, 2018Talla
A kasar a shekara ta 2016 ne dai wannan Malami mai suna Aman Addurrahman ya bada izinin kai wani hari a kasar ta Indonesiya, wanda ke a matsayin hari na faro da kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa a wannan kasa da ke yankin Kudu maso gabashin Asiya.
Kotun dai ta samu babban malamin mai wa'azi a kasar mai suna Aman Addurrahman da laifin kitsa hare-haren da aka kai a kasar da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, wanda a cikinsa maharan guda hudu suka mutu.
Shugaban kotun mai suna Akhmad Zaini, ya kara da cewa an sami wannan malamin kuma da hannu cikin wasu hare-hare da aka kai a kasar. Sai dai Malamin da ke zaune ya yin yanke masa hukuncin bai nuna wani yanayi na nadama ba.