1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sama da 1.400 ne suka mutu a Indonesiya

Salissou Boukari
October 3, 2018

Mutane sama da 1.400 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta wakana a tsibirin Sulawesi na kasar Indonesiya kamar yadda sabon adadi na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar.

https://p.dw.com/p/35u5F
Indonesien Palu Erdbeben und Tsunami zerstört Infrastruktur
Hoto: Getty Images/AFP/J. Samad

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da tarin bukatun gaggawa da ake da su ga mutanen da suka tsira da rayukansu. Kimanin mutane dubu 200 ne dai a halin yanzu ke cikin babbar bukatar agajin gaggawa a cewar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai gula da agajin gaggawa na OCHA, wanda cikinsu akwai dubban yara kanana. An kimanta gidaje dubu 66 da suka ruguje sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.5 a ma'aunin Reshter.

Sai dai tun wannan lokacin wadanda suka tsira da rayukansu na ci gaba da fama da matsalar yunwa ta sabili da rashin abinci, ruwa mai tsafta da dai sauransu. An kuma kiyasta wasu mutanen 113 da suka samu raununa a birnin Palu inda girgizar kasar ta fi kamari.