1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sistani ya magantu a kan rikicin Iraki

Zulaiha Abubakar
November 22, 2019

Fararen hula sun rasa rayukansu sakamakon arangama tsakanin masu kyamar gwamnati da jami'an tsaro a Iraki.

https://p.dw.com/p/3TZJv
Irak | Proteste gegen Regierung
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/H. Mizban

A lokacin da yake hudubar sallar Jumma'a, jagoran musulmi na mabiya mazhabar Shi'a, Ayatollah Ali al-Sistani ya bukaci jam'iyyun siyasa su gaggauta amincewa da dokokin sauyin tsarin mulki kuma su saurari bukatun masu zanga-zanga, domin kawo karshen rikici a kasar. A yanzu dai masu zanga-zangar na rike da bangare guda na  manyan gadoji uku da ke Bagadaza babban birnin kasar wadanda kuma ke zaman hanyar isa fadar gwamnati, duk kuwa da cewar gwamnatin ta jibge jamai'an tsaro domin dakile zanga-zangar .

Tuni Majalisar Dinkin Duniya tare da kasashen Turai suka yi Allah wadai da amfani da karfin da jami'an tsaro ke yi a kokarin dakile masu zanga-zangar.