Iraki: Dubban kananan yara na cikin hadari a Mossul
June 5, 2017Talla
Asusun na UNICEF ya ce yaran da suka hada da maza da mata na cikin babban hadari ne a tsohon birnin Mossul, da kuma sauran wasu yankuna na yammacin birnin, inda suke tsakanin huta biyu ta mayakan IS da kuma dakarun gwamnatin Iraki, sannan hare-haren da ake kaiwa sun shafi har da manyan asibitoci da kuma wasu wuraren kiwon lafiya a cewar UNICEF.
Asusun kula da kananan yaran na UNICEF ya yi kira ga bangarorin biyu da su mutunta dokokin kasa da kasa ta hanyar bada kariya ga wadan an yara da ke neman hanyoyin ficewa daga inda suke. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutane dubu 750 ne suka bar gidajensu tun daga farkon wannan samame na neman kwato birnin na Mossul a watan Oktoban bara.