Iraki: Harin bam ya kashe mutane masu yawa
July 3, 2016Talla
Rahotanni daga birnin na Bagadaza na cewa ai kai harin ne tun da sanyin safiya da wata mota da aka dana wa bam a saman wani titi da ke makare da mutane na unguwar hada-hadar kasuwanci ta Karraga inda tarin jama'a suka zo domin yin cefane kayan sallar azumin Ramadan da ake shirin gudanarwa.
Harin dai ya ruguza gine-gine da dama tare da haddasa tashin gobara a gurare da yama. Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka taba kaiwa birnin na bagdaza a wannan shekara.
Tuni dai Kungiyar IS ta dauki alhakin kan wannan hari wanda ya zo mako daya bayan da sojojin gwamnatin Irakin suka yi nasara fatattakar Kungiyar ta IS dagaa birnin Fallouja da ke a nisan kilomita 50 da birnin na Bagadaza.