1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta hana sojojinta dogaro da Amirka

Abdul-raheem Hassan
February 5, 2020

Gwamnatin Iraki ta ja kunnen sojojinta da su rage neman shawarar dakarun Amirka yayin kaddamar da farmaki kan mayakan IS a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/3XKIe
Irak Kirkuk Kurden-PKK
Hoto: picture-alliance/AA/H. Arslan

Wasu manyan kwamandojin Iraki sun tabbatar da ikirarin gwamnatin yayin da dangantaka tsakanin Washingoton da Bagadaza ke kara tsami, bayan kashe kwamandan sojan Iran Qassem Soleimani a filin jirgin Bagadaza.

A karshen watan Janairun 2020 rundunar sojin Iraki suka ci gaba da hadakar aikin soja a hukumance da sauran dakarun kawancen kasashen waje, bayan dakatar da aiki tare saboda fargabar da yankin Gabas ta Tsakiya ta shiga kan kisan Janar Soleimani.