Iraki ta kaddamar da harin kwato Mosul
October 17, 2016Mahukuntan Iraki sun sanar da cewa dakaran gwamnatin kasar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyin mayaka sun kaddamar a wannan Litinin da gagarimin harin neman kwato birnin Mosul daga hannun mayakan Kungiyar IS. Firaministan kasar ta Iraki Haider al-Abadi ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya gabatar a tashar talabijin ta gwamnatin kasar:
"Ya ce al'umma mai daraja ta Iraki, a yau lokacin nasararmu ya yi, mun kaddamar da gagarimin harin kwato birnin Mosul. Nan ba da jimawa ba, da yardar Allah za mu kasance a tare a birnin Mosul mu gudanar da binkin murnar kwato shi inda rayuwa za ta kasance ba tare da Kungiyar IS ba."
Dama dai yau watanni da dama kenan da dakaran gwamnatin Iraki da sauran kungiyoyin mayaka masu goya masu baya suka ja daga a kusa da birnin Qayyarah mai nisan kilomita 60 da birnin na Mosul birni na biyu na kasar ta Iraki da ke kunshe da mutane miliyan daya da rabi. Sai dai kimanin mayakan Kungiyar IS dubu biyar ne dauke da manyan makaman yaki suka ja suma tasu daga a cikin birnin na Mosul wanda suka kwace a cikin watan Yunin shekara ta 2014.