Iraki ta mikawa Turkiyya yaran IS 200
May 29, 2019Talla
Wata kotu a Iraki ta tabbatar da mika yaran da IS suka bari a kasar kusan 200 ga hukumomin kasar Turkiyya bayan ayyana murkushe mayakan IS a watan Disamban 2017. Kungiyar IS ta shafe kusan shekaru uku suna rike da iko a wasu yankunan arewacin Iraki, amma duk da ikirarin gwamnati suna kai harin sari ka noke da yin garkuwa da mutane a sassa dabam-dabam.