Iraki za ta bawa Kurdawa kariya
September 30, 2017Haidar al-Abadi ya wallafa a shafinsa na twitter cewa " Za mu kare 'yan uwanmu Kurdawa kamar yadda muke bawa saurarn fararen hula a Iraki kariya, ba za mu taba bari a ci mutuncin 'yan uwanmu ko ta wane hanya ba, ba za mu zuba idanu muna kallo a kawo musu hari ba mu karesu ba."
To sai dai wannan ikirari na Firaiministan na zuwa ne a dai-dai lokacinda gwamnatin Iraki, ta kaddamar da girke rundunar sojin hadin gwiwa da Turkiyya a kan iyakar kasar.
Yankin Kurdawan dai na ci gaba da fuskantar wariya tun bayan da suka jefa kuri'ar raba gardama da neman 'yanci a ranar Litinin da ta gabata. A yanzu dai kasashe da ke makota irin su Iran da Turkiyya na cikin kasashen da suka dauki matakan katse huldar kasuwanci da zirga-zirgan jiragen sama a yankin kurdawan.