Iraki ta haramta dangantaka da Isra'ila
May 27, 2022Dokar ta samu amincewar 'yan majalisu 275 cikin 329, inda suka kare matsayarsu da cewa shi ne zahirin abin da 'yan kasar Iraki ke bukata. Sai dai tuni gwamnatin Amirka ta yi tir da wannan doka, tare da yin gargadin cewa dokar barazana ce ga ci gaban kasar da kuma takaita 'yancin dan Adam da haddasa fargaba ga kasashe makwabta.
Dama dai Iraki ba ta amince da Isra'ila ba tun kafuwar kasar a shekarar 1948, wannan ya sa kasashen biyu ba su da dangantakar diflomasiyya.
A farkon shekarar 2022, Iran ta harba makami mai linzami guda 12 zuwa birnin Irbil da ke arewacin kasar Kurdawa da zimmar kai farmaki kan sansanin leken asirin Isra'ila.
Rahoton kwamitin bincike na majalisar dokokin Iraki ya ce ba a sami wata hujja da za ta goyi bayan zargin da Iran ta ke yi na cewa akwai sansanin leken asirin Isra'ila a Irbil ba.