Iraki:An dakatar da Zaben raba gardama na Kurdawa
September 18, 2017Talla
Wata sanarwa gwamnatin ta Iraki ta ce an dakatar da zaben ne har sai an bincike wasu korafe-korefen da aka shigar a game da zaben wanda wasu ke cewar ya sabama kaidar kudin tsarin mulkin. Wasu majiyoyin sun ce 'yan majalisu akalla guda takwas ne na 'yan Shi'a da Turkumenes wasu tsirarun kabilun da ke a arewacin Bagadaza suka shigar da karan a game da zaben wanda suka ce ya sabama doka.