1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi tir da takunkumin Amirka

Abdourazak Maila Ibrahim MAB
October 4, 2022

Kasar Iran ta yi Allah wadai da abin da ta kira munafuncin shugaban Amirka Joe Biden, kwana guda bayan sanar da sabbin takunkuman da Amirka ta kakaba wa Tehran saboda murkushe masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/4HjLQ
Iran | Präsident Ebrahim Raisi vor dem Abflug zur UN Generalversammlung
Shugaban Iran Ebrahim Raisi gabanin zuwa taron Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Vahid Salemi/AP/picture alliance

A lokacin da ya yi bayyani a shafinsa na Instagram, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanani ya ce "Ya kamata Joe Biden ya yi tunani game da yadda kasarsa Amirka ta kare hakkin bil'adama kafin ya yi magana kan halin da ake ciki a Iran."

Akalla mutane 92 ne aka kashe a Iran tun lokacin da aka fara zanga-zangar yin tir da mutuwar Mahsa Amini, a cewar kungiyar kare hakkin bil adama, yayin da hukumomi suka ce adadin wadanda suka mutu bai fi 60 ba ciki har da jami'an tsaro 12.

Dama dai jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Ali Khamenei, ya soki manufar Washington a jiya litinin, yana mai zargin Amirka da Isra'ila da ruruta wutar zanga-zanga da ta kasance mafi muni a Iran a cikin shekaru ukun da suka gabata.