1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Iran za ta soke takunkumin hana amfani da WhatsApp

December 24, 2024

Shekaru biyu bayan kisan matashiya Masha Amini, mahukuntan Iran na shirin dage takunkumin da suka saka na haramta yin amfani da wasu kafafen sadarwar zamani.

https://p.dw.com/p/4oYhn
Logo | Meta Konzern
Hoto: Jens Büttner/dpa/picture alliance

Majalisar koli mai lura da kafafen sadawar zamani ta Iran ta kada kuri'ar amincewa da dage dokar haramcin yin amfani da manhajar WhatsApp wadda aka toshe yau sama da shekaru biyu kenan.

Kamfanin dillacin labarai na IRNA mallakar gwamnatin Iran ya ruwaito cewa daukacin 'yan majalisar ne suka amince da soke haramcin a matsayin share fage na dage takunkumin da mahukuntan kasar suka kakaba wa WhatsApp da Google Play. 

Idan za a iya tunawa dai fadar mulki ta Tehran ta dauki matakin toshe wadannan kafafe sadarwar zanmani da aka fi amfani da su a kasdar ne a shekarar 2022, a lokacin da bore ya barke a bayan kisan marigayiya Mahsa Amini.