IS na kokarin kame rijiyoyin mai a Libiya
January 5, 2016Rahotanni daga kasar Libiya na cewa mayakan Kungiyar IS sun kara kaddamar da harin bam a wannan Talata a kusa da tashar jiragen ruwan dakon man fetur ta Es Sider ta kasar Libiya. Kakakin hukumar tsaron kamfanin man fetir na kasar ta Libiya ya bayyana cewa daya daga cikin tankunan man ya kama da wuta.
Ya kuma kara da cewa a halin yanzu mayakan Kungiyar ta IS na a tazarar kilomita 30 zuwa 40 ne kawai da tashar jiragen ruwan dakon man fetur din ta kasar ta Libiya.Jami'an rindunar tsaron tashar jiragen ruwan dakon man fetur ta kasar ta Libiya bakwai ne dai suka mutu a yayin da wasu 25 suka ji rauni a lokacin harin farko da Kungiyar ta IS ta kaddamar a jiya Litanin. Kungiyar IS wacce ta kwace iko da birnin Syrte na gabar tekun Bahar Rum na kokarin kame rijiyoyin mai na kasar ta Libiya ne.