1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS na sa yara yin harin kunar bakin wake

September 8, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mayakan kungiyoyi masu kaifin kishin addini a Iraki sun hallaka yara tare kuma da amfani da karin wasu a matsayin 'yan kunar bakin wake.

https://p.dw.com/p/1D8zq
Syrien Kindersoldaten Archiv 2013 Aleppo
Hoto: Guillaume Briquet/AFP/Getty Images

Mukaddashiyar babban sakataren Majalsiar ta Dinkin Duniya Leila Zerrougui da ke kula da harkokin kananan yara da rikice-rikice masu nasaba da makamai ta ce kimanin yara dari bawai ne aka kashe a Irakin daga farkon shekarar nan zuwa yau.

Ms. Zarrougui ta ce kungiyar nan da ke rajin kafa daular musuluci wato IS ta dauki yara kanana aiki wasunsu ma ba su wuce shekaru 13 inda ake basu manya makamai don gadin wurare da kuma kame fararen hula, yayin da a hannu guda ake amfani da wasunsu a matsayin masu kai harin kunar bakin wake.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a dazu kwamitin sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya ya gabatar da wani taro da ma tafka mahawara kan sanya yara aikin soji a kasashen da suka hada da Libya da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Afgahnisatan gami da Sudan ta Kudu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu Waba