1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta ce ta hallaka sojojin Najeriya 10

Zulaiha Abubakar
March 2, 2019

Kungiyar nan ta IS da ke rajin girka daular Islama a wasu kasashen duniya ta sanar da kai harin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojojin Najeriya 10.

https://p.dw.com/p/3EMum
Irak Islamischer Staat Propagandafoto
Hoto: picture-alliance/Zuma Press

A wata sanarwa da ta fidda dazu, kungiyar ta ce ta kai harin ne a garin Tdmari da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar cikin wannan mako kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya shaida.

Wani bangare na kungiyar da ke gwagwarmaya a yammacin Afirka wato ISWA wanda a baya yake tare da kungiyar nan ta Boko Haram ya kara kaimi wajen kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriyar duk kuwa da cewar gwamnatin kasar na ikirarin magance ayyukan ta'addanci a wannan yanki.