IS ta dauki alhakin harin Belgium
October 17, 2023Wani mutum ya bayyana kansa a matsayin dan kungiyar IS, ya dauki alhakin kai harin a wani faifan bidiyo da aka wallafa a yanar gizo. Ya zuwa yanzu kwararru na bincike kan sahihancin bidiyon.
"Dole ne 'yan ta'adda su fahimci cewa ba za su taba yin nasara a cikin aniyarsu ba. Ba za su taba iya murƙushe al'ummominmu masu 'yanci da ƙiyayyarsu da tashin hankalinsu ba. Suna nuna rashin ƙarfi ne kawai. Ta'addanci ba zai taba cin galaba a kan mu ba. Yakin da muke fada tare kenan. Kuma muna fada tare da abokanmu na Sweden." a cewar Firaiministan Beljium Alexander De Croo.
Kasar Sweden na fuskantar baraza a ciki da waje, tun bayan da wani dan gudun hijira dan asalin kasar Iraki ya kona Alkur'ani a kasar, matakin da ya harzuka musulman duniya tare da yin barazana daga kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.