IS ta dauki alhakin harin birnin Santanbul
January 2, 2017Hukumomin tsaro a kasar Turkiya na ci gaba da farautar mutumin da ake zargi ya kai wannan hari da ya hallaka kusan mutane 40, kana wasu masu yawa suka samu raunuka, harin da yanzu haka tsagerun IS suka dauki alhakin kai wa inda shugaban kungiyar Abu Bakr Al-Baghdadi ke cewa martani ne daga dakarun Ubangiji.
Tun farko kafofin yada labarai na Turkiya sun ce hukumomi sun yi imanin kungiyar IS mai ikirarin neman kafa daular Islama tana da hannu wajen kai harin na Santanbul, kuma akwai yuwuwar dan bindigan ya fito ne daga kasashen tsakiyar Asiya, tsakanin Uzbekistan ko kuma Kyrgyzstan. A cewar Meir Javadanfar masani kan harkokin kasashen Gabas ta Tsakiya hare-haren sun raunana tattalin arzikin kasar:
"Haka abubuwa da suke faruwa sun janyo rashin kwanciyar hankali na siyasa amma haka ya fi shafan tattalin arziki. Hare-haren ta'addanci da ake samu sun kassara tattalin arzikin Turkiya fiye da yadda ake tsammani kan harkokin siyasa."
Tuni aka fara binne mutanen da lamarin ya ritsa da su, yayin da a hannu daya ake ci gaba da bincike domin bankado wadanda suke da hannu cikin harin. Sai dai abin kuma da ake kara tattaba shi ne Turkiya za ta kara rasa kudaden shiga ta fannin yawon bude ido da zuba jari a wasu fannoni masu muhimmanci, kamar yadda Meir Javadanfar masanin harkokin kasashen Gabas ta Tsakiya ya yi karin haske:
"Idan aka samu yunkurin juyin mulki da kame-kamen mutane masu yawa, dubban mutane, haka zai gurgunta tattalin arziki. A shekarar da ta gabata a karon farko tattalin arzikin Turkiya ya koma da baya."
Masanin ya kara da cewa ana kara samun rashin aiki, kana masu matsananci ra'ayi su na karuwa, saboda rashin masu zuba jari da zai zaburar da tattalin arzikin kasar. A shekarar da ta gabata ta 2016 an samu hare-haren da suka janyo mutuwar daruruwan mutane, kuma sabon harin yayin da ake bikin shiga wannan sabuwar shekara ta 2017 Miladiya, na nuni da cewa akwai yuwuwar ba ta sauya zani ba, kan abubuwan da mutanen Turkiya za su fuskanta cikin sabuwar shekarar.