1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta dauki alhakin harin da aka kai a Jami'ar Ohio

Abdul-raheem Hassan
November 30, 2016

Kungiya IS ta bayyana Abdul Razak Ali Artan mai shekaru 20 da ya kai hari da wuka a jami'ar Ohio ta ksar Amirka da cewa sojanta ne, wanda dama hukumomin tsaron Amirka ke zargin yana da tsattsauranra'ayin addini.

https://p.dw.com/p/2TUrn
USA Ohio State University Campus in Columbus
Hoto: Reuters/thelantern.com/C. Hass-Hill

An dai ci gaba da bibiyar shafukan sada zumunta da maharin ke amfni da su kamin ya kai harin don binciko hakikanin dangantakarsa da kungiyoyin 'yan ta'adda. Kungiyar IS ta ce sun yi alfahari da harin a matsayin jan kunne ga Amirka a kan yadda ta ke tsoma baki a lamuran da suka shafi addinin Musulunci a ciki da wajen kasar, musamman kan yadda sojojinta ke taka rawar gani a rundunar hadin guiwa da ke yakar IS a wasu kasashen duniya.

Wasu bayanai da ke cin karo da juna dai, na cewa jami'an 'yan sanda na nesanta kansu da bindige maharin da ya kutsa kai cikin mota kana ya fara kai sara kan dandazon mutane a jami'ar ta Ohio. A yanzu dai dalibai sun koma daukar karatu a cikin jami'ar bayan da aka jibge jami'an tsaro da zasu kare duk wani rudani da zai daga hankalin al'umma.