IS ta kai hari ga ma'aikatun mai a Libiya
February 22, 2016Talla
Wannan labari ya fito ne a ranar Litinin (22.02.2016) daga Moustafa Sanalla da ke a matsayin shugaban ma'aikatar man fetir ta kasar ta Libiya ta NOC (National Oil Corporation). Ma'aikatar man ta Fida dai na a Kudu maso yammacin wasu ma'aikatun na man da suka hada da na Sider da kuma na Ras Lanouf da su ma suka fuskanci hare-haren ta'addanci daga 'yan kungiyar ta IS tun a watan Janairu da ya gabata.
Kasar ta Libiya dai ta yi zaman fitar da danyan man da ya kai ganga dubu 360 zuwa dubu 370 a ko wace rana kafin tashin hankalin da ya kifar da gwamnatin marigayi Shugaba Mohamar Kadhafi a shekara ta 2011.