Hari kan gangamin siyasa a Pakistan
July 13, 2018Talla
Kamfanin dillancin labarai na Amaq da ke yada farfagandar kungiyar, ya bayyana cewa IS din ce ke da alhakin kai harin na kunar bakin wake da aka kai a garin Mastung da ke gundumar Balochistan da ya hallaka mutane sama da 80. Harin wanda ke zaman mafi muni da aka kai kan gangamin siyasa a baya-bayan nan a Pakistan din, na zuwa ne gabanin babban zaben kasar da za a gudanar a ranar 25 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.