IS ta kashe farar hula 30 a birnin Al-Bab
December 26, 2016Talla
Rundunar sojin kasar ta Turkiyya ta ce mayakan Kungiyar ta IS sun halaka mutanen ne a jiya Lahadi a lokacin wani hari da suka kai masu. Makonni da dama kenan da da sojojin kasar ta Turkiyya da hadin gwiwar 'yan tawayen Siriya suka kaddamar da farmaki kan birnin na al-Bab wanda suke neman kwacewa daga hannun Kungiyar ta IS da har yanzu ke ci gaba da yin turjiya.
Ko a ranar Larabar da ta gabata dai mayakan Kungiyar ta IS sun halaka sojojin Turkiyya 16 wanda ya zama barna mafi girm da mayakan Kungiyar ta IS suka taba yi wa sojojin Ankarar tun bayan soma fadan a watan Agustan da ya gabata.