IS ta sace 'yan kasar waje a Libiya
March 9, 2015Talla
Mai magana da yawun ma'aikatar ta ce 'yan IS din ba su illata mutanen da suka kame ba kuma sanda suka kame su din dukanninsu na cikin koshin lafiya.
Mutanen dai sun hada ne da 'yan kasar ta Austriya da Jamhuriyar Czech da Bangladesh da Philippines da kuma wani dan Afrika da ba a tantance ko dan wace kasa ba ne. Ya zuwa yanzu dai IS ba su ce komai ba game da sace mutanen.
A baya dai kungiyar ta sace 'yan kasashen ketare da dama inda ta hallaka kusan dukanninsu ta hanyar yi musu yankan rago kamar yanda su kan nuna a faifan bidiyon da suke fiddawa.