An ji wata rauni a yayin bikin ranar mata
March 8, 2019Talla
Rikici ya barke inda har aka raunata wasu daga cikin matan. Kungiyoyi daban-daban masu rajin kare hakkokin mata ne suke gudanar da ayyukansu a karkashin kungiyar hadaka ta Neshot Hakotel da ke cika shekaru talatin da kafuwa.
Bayan hatsaniyar da aka tura jami'an tsaron Isra'ila don shawo kanta, matan sun ci gaba da sha'anin bikin kamar yadda suka tsara.Taken bikin na bana, shi ne daidaita gudunmuwar maza da mata ga ci gaban kasa kuma har yanzu dai mata na can baya a fannoni daban daban kamar yadda bincike ya nunar.