1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: An zabi sabon shugaban kasa

June 2, 2021

Akwai yiyyuwar komawa rumfunan zabe a Isra'ila idan har 'yan adawa su ka gagara cimma matsaya ta hada ka a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3uLqj
Israel neu gewählter Präsident Izchak Herzog
Hoto: Manuel Balce Ceneta/AP/dpa/picture alliance

'Yan adawa a Isra'ila sun shiga matakin karshe a wannan Larabar wajen yin hada ka domin tunkude firaministan kasar mai ci yanzu Benjamin Netanyahu daga karagar mulkin da ya kwashe shekaru goma sha biyu ya na murza zarensa.

Yair Lapid da Naftali Bennett na aiki tukuru wajen ganin hakarsu ta cimma ruwa, bayan da Lapid din ya samu cikakken goyon baya daga Bennett mai ra'ayin rikau kuma dan kishin kasa. Sai dai idan yunkurin na su ya gaza cimma gacci to la budda za a koma runfunan zabe wanda hakan ka iya bai wa shugaba Netanyahu damar ci gaba da jagorancin kasar ta Baniyahudu.

Haka zalika a yau din nan, majalisar dokokin kasar ta zabi Isaac Herzog a matsayin sabon shugaban kasa wanda zai fara aiki a ranar 9 ga watan Yuli mai zuwa.