1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ba ta neman kujera a kwamitin MDD

Yusuf Bala Nayaya
May 5, 2018

Yayin da kasar Isra'ila ke fama da fafutika gabannin zabe a watan Juni, ta bayyana cewa ta fice daga jerin kasashe da ke muradin kujerar jagoranci a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/2xDFl
USA UN-Sicherheitsrat - Syrienkonflikt
Hoto: picture alliance/Xinhua/L. Muzi

Isra'ila dai na cikin jerin kasashe uku da ke muradin kaiwa ga kujeru biyu a wannan kwamiti mai karfin fada a ji a Majalisar Dinkin Duniya daga watan Janairu. Sauran kasashen kuwa su ne Jamus da Beljiyam.

Kwamitin Sulhun dai na da mambobi biyar na din-din-din wato Amirka da Rasha da China da Birtaniya da Faransa sannan mambobi goma da ake zaba bayan kada kuri'ar mambobi 193  inda su kan yi wa'adin karba karba na shekaru biyu-biyu. Janyewar ta Isra'ila dai ta ba wa Jamus da Beljiyam tabbacin samun kujerun biyu a zaben da za a yi a ranar 8 ga watan Yuni.