1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ba za ta cire shingen da ta yiwa Gaza ba

June 3, 2010

An yi jana'izar mutanen da suka rasu a harin da Isra'ila ta kai kan jiragen ruwan agajin Gaza a birnin Istanbul

https://p.dw.com/p/NgmZ
Hoto: AP

Gwamnatin Turkiya ta tabbatar da cewa 'yan ƙasarta takwas da Ba-Amirke ɗaya ɗan asalin ƙasar ta Turkiya aka harbe har lahira a farmakin da Isra'ila ta kai kan wani ayarin jiragen ruwan dake ɗauke da kayan agaji ga Gaza. Wata sanarwa daga ofishin Firaminista Recep Tayyip Erdogan ta ba da asalin dukkan mutane su tara dukkansu maza masu shekarun haihuwa daga 19 zuwa 61. Sanarwar ta ci-gaba da cewa an miƙa gawarwakin mutanen ga iyalansu bayan an gudanar da bincike kansu a birnin Istanbul. Yanzu haka dai an yi jana'izar mutane takwas daga cikin waɗanda suka rasu a harin da Isra'ilar ta kai kan jiragen ruwan agajin Gaza a birnin Istanbul. Ƙasashen duniya da dama sun yi tir da harin da Isra'ilar ta kai kan ayarin jiragen ruwan. A halin da ake ciki babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon yayi kira ga Isra'ila da ta ɗage ƙofar ragon da ta yiwa Zirin Gaza nan-take.

"Wannan al'amarin ya nunar a fili babbar matsalar dake akwai. Ci-gaba da rufe kan iyakokin Zirin Gaza, babban kuskure ne dake mayar da hannu agogo baya. Jan kunnen farar hula ne da ba su san hawa ba su san sauka ba, shi ya sa ya zama dole hukumomin Isra'ila su janye wannan mataki."

To sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da kiraye-kirayen na ya ɗage ƙawanyar da ƙasar Yahudun Isra'ila ta shafe shekaru uku tana yiwa Zirin na Gaza.

A wani labarin kuma Afirka Ta Kudu za ta kira jakadanta daga Isra'ila domin nuna rashin jin daɗinta ga matakin da Isra'ilan ta ɗauka kan jiragen ruwan kayan agajin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi