Cinikin makamai tsakanin Isra'ila da Amirka
December 31, 2021Talla
Ma'aikatar tsaron Isra'ilar ta ce ta kulla wannan yarjejeniya domin siyan jirage masu saukar ungulu kirar CH-53K guda 12 da kuma jiragen sama masu jigilar mai kirar Boeing KC-46 guda biyu. Ana sa ran a mika helikwaftocin ga Isra'ila nan da shekarar 2026, sai dai Amirka na duba yiwuwarkai jiragen Isra'ila a shekarar 2024.
Kulla yarjejeniyar na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da wani rahoton cibiyar nazarin zaman lafiya ta duniya ya yi nuni da cewa masana'antar kera makamai ta duniya na bunkasa duk da nakasun da annobar coronata yi a fanoni dabam-dabam. Kafafon yada labaran Isra'ila dai na hasashen cewa jiragen na dakon mai, ka iya kasancewa kan gaba wajen kai farmaki a cibiyoyin nukiliyar Iran da aka dade ana yi.